An samu tashin hankalin ne a yankin Um-Rakoba na jihar East Darfur tsakanin kabilar Rizeigat da ta Maalia. Wani jami'i a wurin ya bayyana cewa, a safiyar jiya, dakaru kimanin 3000 daga kabilar Rizeigat suka kai hari kan yankin Um-Rakoba. Daya daga bangarorin biyu suka yi amfani da manyan makamai wajen kai ma juna hari sai dai Kuma kuma an tarar da takardun shaida na jami'an soja a jikin gawawwaki 7.
Wadannan kabilu biyu sun taba gwabzawa da juna tun farko a ranar 11 ga wata, wanda ya haddasa mutuwar mutane sama da 100. Bisa kokarin gwamnatin Sudan na shiga tsakani, sarakunan kabilun biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta a ranar 13 ga wata.(Fatima)