Sanarwar ta kara da cewa kasar Sudan na kokarin tsoma hannu cikin harkokin gidan Libya, ta hanyar goyon bayan mayaka 'yan ta'adda a kasar, wanda hakan kai tsaye ya keta hurumin kasar ta Libya. Sanarwar ta kuma bayyana cewa, tuni gwamnatin wucin gadin kasar ta bukaci jami'an sojin Sudan da su koma kasarsu.
A daya hannun kuma, kasar Sudan ta gaskata cewa ita ce ta aike da wani jirgin sama na soja zuwa kasar ta Libya, amma ta ce jirgin na dauke ne da wasu kayayyakin da sojoji masu aikin sintiri na kasashen biyu dake yankin kan iyakar kasashen ke bukata. (Maryam)