Bisa labarin da jaridar New York Times ta kasar Amurka ta bayar a kan yanar gizonta, an ce, wannan ne karon farko da cikakken zaman kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya mai da tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka a matsayin babban taken taron, kwaskwarimar da aka yi game da dokokin kasa za su kyautata tsari da yanayin adalci na dokokin kasar Sin yadda ya kamata.
Haka zalika, jaridar Les Echos ta kasar Faransa ta ba da labarin cewa, a yayin taron, an tattauna kan yadda za a iya tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka, inda aka kuma fitar da matakai da dama dangane da aikin, lamarin ya nuna aniyar jam'iyyar kwaminis ta Sin sosai kan yin kwaskwarima a kasar. (Maryam)