in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Raya kasar Sin bisa tsarin gurguzu ya dogara ga dokokin kasar
2014-10-24 15:47:23 cri

A yau Jumma'a 24 ga wata, jaridar People's Daily ta wallafa wani sharhi mai taken "cimma burin samun babban ci gaba kan aikin tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka", inda aka nuna cewa, raya kasar Sin irin na gurguzu ya dogara ne ga aikin tafiyar da harkokinta bisa doka. Kana farfadowar al'ummar Sin tana dogara ne ga tabbacin da aka samu a wannan fanni.

Sharhin ya bayyana cewa, a jiya Alhamis 23 ga wata aka rufe cikakken zama na 4 na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 18, inda aka zartas da wani kuduri dangane da wasu muhimman batutuwa kan yadda za a kara inganta matakan tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka daga dukkan fannoni..

Kudurin ya zayyana matsalolin da kasar Sin ke fuskanta a fannin tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka, da gabatar da burin da za a cimma da kuma ka'idojin da za a bi a wannan fanni. Sa'an nan ya gabatar da wasu sabbin ra'ayoyi da matakan tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka. Bugu da kari ya amsa wasu tambayoyi game da dangantakar dake tsakanin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta Sin da aikin tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka. Haka zakila ya gabatar da wasu shirye-shirye a fannonin kafa dokoki, gudanar da ayyuka bisa doka, yin shari'a cikin adalci, sanya jama'a su bi dokoki da dai sauransu, wanda ya amsa kiran da jama'ar kasar suka yi da kulawar da suke nunawa. Hakan zai kara azama sosai ga yunkurin tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China