Daga watan Yunin bara zuwa watan Satumban bana, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kaddamar gudanar da wani aikin horaswa mai taken 'Kulawa da jama'a da gudanar da hakikanin aiki da yaki da cin hanci da rashawa'. A Jiya Laraba 8 ga wata, babban darakta na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, bisa wannan aiki, an kara kafa mutuncin jam'iyyar a zuciyar jama'a, ta yadda jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kara hada jama'arta a gu daya, a kokarin kara sa kaimi ga yin kwaskwarima da samun bunkasuwar kasar. Don haka in ji shi dole ne JKS ta kara sa kula ga ayyukanta wadanda ke cikin mawuyacin hali.
An kaddamar da taron yin sharhi kan wannan aiki a jiya a nan birnin Beijing, inda shugaba Xi ya jaddada cewa, dole ne a kara sa kulawa a kanga jam'iyyar yadda ya kamata, wannan ne darasi da aka samu ta wannan aiki. Dole ne duk membobin JKS su ci gaba da kokari a wannan fanni ba tare da kasala ba a ko da yaushe.(Fatima)