Bisa kudurin da aka tsai da a yayin taron hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, an ce, daga yau ranar 20 ga wata, har zuwa ranar 23 ga wata, za a gudanar da cikakken taro karo na 4 na kwamitin tsakiya na 18 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a nan birnin Beijing, yayin taron, za a tattauna babban batu game da yadda za a kara kyautata aikin tafiyar da harkokin kasa bisa doka daga dukkan fannoni a kasar. Wannan babban aiki ne da ake yi a kasar Sin wajen ci gaban kwaskwarimar siyasa, a matsayin wani babban aikin dake da ma'anar gaske.
Alamu sun nuna cewa, yayin wannan cikakken taron, za'a mai da hankali sosai kan batun tafiyar da harkokin kasa bisa doka, wanda ba a taba ganin irinsa a tarihin mulkin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Ra'ayin jama'ar kasa na ganin cewa, a halin da ake ciki yanzu, lokaci ya yi na kara zurfafa kwaskwarima a kasar Sin daga dukkan fannoni, haka ma tafiyar da harkokin kasa bisa doka na da muhimmanci kwarai da gaske. An ce, ya kamata kasar Sin ta yi amfani da tsarin da ya dace domin yaki da cin hanci da rashawa, ta yadda za a iya tabbatar da zaman al'umma cikin karko, tare da ingiza bunkasuwar tattalin arzikin kasar. (Jamila)