Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Reuters ya bayar, an ce, matakan da aka zartarwa a yayin taron suna da babbar ma'ana ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, wadda ta kasance kasa ta biyu mai ci gaban tattalin arziki a duniya. Ban da wannan, Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta jaddada muhimmancin kyautata tsarin gudanar da tsarin mulkin kasa da sa ido a kai, da tsarin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da zaunannen kwamitinta na sa ido kan tsarin mulkin kasa.
Haka zalika kuma, kamfanin dillancin labaru na The Associated Press ya bayar da labari cewa, a cikin sanarwar da JKS ta bayar bayan taron, ta ce, za ta tafiyar da harkokin kasa bisa tsarin mulkin kasar da dokokin kasar, sa'an nan za ta hana a yi katsalandan kan batutuwan da suka shafi harkokin shari'a.
Ban da wannan kuma, kamfanin dillancin labaru na AFP ya ba da labari cewa, a yayin taron, JKS sanar da cewa, za ta ci gaba da bin hanyar gurguzu mai tsarin musamman ta hanyar tafiyar da harkokin kasa bisa doka, da kafa tsarinta na tafiyar da harkokin kasa bisa doka, kana da raya kasa mai bin tsarin gurguzu da ke tafiyar da harkokin kasa bisa doka. Babu shakka wannan taro ya tsara wani kundi ga kasar Sin kan yadda za ta tafiyar da harkokinta bisa doka. (Zainab)