in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Batun bincikar tsohon jigo a JKS na nuni ga manufar ta ba-sani-ba-sabo
2014-07-30 14:32:07 cri

Mahukunta a nan kasar Sin sun bayyana aniyar bincikar daya daga tsaffin kusoshin JKS Mr. Zhou Yongkang, sakamakon zargin da ake yi masa na karya ka'idojin ayyukan hukuma.

Sanarwar fara binciken Zhou wadda aka fitar a ranar Talata dai, na nuni ga yadda jam'iyyar ta kwaminis ke kokarin aiwatar da manufofin kakkabe cin hanci da rashawa daga sassan ayyukan gwamnati, ta hanyar daukar matakan ba-sani-ba-sabo, kan duk wani wanda ya taka doka.

Manazarta dai na ganin gurfanar Zhou gaban kwamitin bincike da ladabtarwar jam'iyyar ko CCDI a takaice, duk da kasancewarsa tsohon mamba a hukumar siyasa ta kwamitin tsakiyar JKS, na haskakawa al'ummar Sinawa cewa, babu wani mutum da ya fi karfin doka, komai kuwa matsayinsa a jam'iyya, ko mataki na gwamnati.

Wasu rahotanni daga CCDI din sun bayyana cewa, daga watan Nuwambar shekarar 2012 ya zuwa yanzu, kimanin jami'ai 40 daga larduna da ma'aikatun hukuma ne aka bincika, game da laifuka masu alaka da cin hanci da rashawa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China