in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana kan hanya mai dacewa
2014-10-16 15:39:19 cri

Memban hukumar harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma sakataren sakatariyar kwamitin tsakiya kana ministan kula da harkokin fadakarwa na kasar Sin Liu Qibao zai gabatar da sharhin da ya rubuta mai taken "Kasar Sin tana kan hanya mai dacewa---ra'ayoyina game da hanyar bunkasa Sin mai halayen musamman na gurguzu" a mujallar "neman gaskiya" ta kasar Sin.

A cikin sharhin, Liu Qibao ya bayyana cewa, bayan yakin duniya na biyu, musamman a shekaru fiye da 30 da suka gabata, kasar Sin ba ta bi tsohuwar hanyar rufe kofa ba, kana ba ta bi hanya mai kuskure wajen canja tsari ba, kasar Sin tana bin sabuwar hanyar bunkasa kasa mai halayen musamman na gurguzu. A wannan hanya, kasar Sin ta yi dauki shekarun da ba su zarce goma ma kawai wajen cimma burinta yayin da kasashe masu ci gaba suka yi shafe shekaru fiye da dari daya wajen cimma irin wannan buri, Sin ta daidaita matsalolin da suka shafi abinci da tufaffi da kuma yin kokarin samar da wadata ga dukkan al'ummar kasar, kasar Sin tana fuskantar kyakkyawar makoma ta samun babban ci gaba. Kasar Sin ta bunkasa daga kasa mai rashin isassun kayayyaki zuwa kasa mai karfin masana'antu a duniya da kuma kasar da ke kusa da tsakiyar duniya.

Yadda aka kafa hanyar bunkasa Sin mai halayen musamman ya bayyana cewa, ana samun isassun kayayyaki da kyautatuwan tsari a kasar, kana ana samun farfadowar al'adu a kasar. Game da farfadowar al'adu a kasar Sin, abu mafi muhimmanci shi ne yada ra'ayoyin son kasar, da yin kwaskwarima da kirkire-kirkire, suka zama ra'ayin musamman na kasar Sin. A wannan hanya, kasar Sin ta bunkasa abubuwan da suka shafi al'adu ta fannoni daban daban, kamar wasan kwaikwayo, kide-kiden kabilu, rubutattun labarai, wakoki, fina-finai, wasan kwaikwayo na telebijin, kide-kiden zamani da dai sauransu. Duk da wadannan nasarori da aka samu ana ci gaba da kara kirkiro fannoni daban daban na al'adu, kana jama'a suna sha'awar abubuwan da suka shafi al'adu daban daban, ta haka tunaninsu zai samu karuwa.

Sinawa mutane ne masu son rayuwa da son cimma burinsu, da samun kyakkyawan ilmi, da aikin yi, da wurin zama mai kyau, da girmamawa, da samun nasarori a ayyukansu da harkokinsu na rayuwa. A cikin shekaru 30 da kasar Sin ta bude kofarta ga kasashen waje da yin kwaskwarima a cikin gida, kasar Sin ta cimma burinta bi da bi, sannan ana ci gaba da yin kokarin kara cimma sabbin burin da aka sanya a gaba. Kasar Sin ta yi shafe shekaru fiye da goma tana kokarin cimma burin kafa tsarin ma'aunin zaman rayuwa mafi kankanta, tsarin inshorar kula da tsofaffi a birane da kauyuka da kuma tsarin kiwon lafiya a dukkan kasar, a inda wasu kasashe yammacin duniya suka shafe shekaru kimanin dari daya kafin su cimma wannan burin. Ya zuwa yanzu kuma, fiye da mutane miliyan 600 ne suka rabu da talauci a kasar Sin, wanda ya cimma kashi fiye da 70 cikin dari na burin kawar da masu fama da talauci a duniya. Bayan da aka yi taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 18, an kyautata tsarin rajistar jama'a, tsarin jarrabawa, da manufar kayyade yawan al'umma, kuma an gabatar da wasu manufofin kyautata zaman rayuwar jama'a, wadanda suka amfanawa jama'ar kasar sosai. Wani masanin kasar Amurka ya yi tsammani cewa, a tarihin dan Adam, ba a taba samun mutane masu yawa a duniya da suke samun rayuwa cikin sauri kamar a kasar Sin ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China