in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ganawa tsakanin manyan jami'an Sin da Amurka
2014-10-21 15:06:02 cri

Mamba mai kula da harkokin kasar Sin Mr. Yang Jiechi ya gana da jami'a mai ba da shawara ga shugaban kasar Amurka kan aikin tsaro Madam Susan Rice a ran 20 ga wata a Washington, fadar mulkin kasar Amurka, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra'ayi kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, gami da wasu batutuwan duniya da na shiyya-shiyya da suka fi jawo hankulansu.

Mr. Yang ya bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu na samun ci gaba sosai bisa kokarin da suka yi. A wata mai zuwa, shugaban kasar Amurka Barack Obama zai harlarci kwarya-kwaryar taron kungiyar hadin gwiwa kan tattalin arziki na nahiyar Asiya da yankin tekun Pacific APEC da za a yi a birnin Beijing na kasar Sin. Sin za ta ci gaba da inganta hadin kanta da kasar Amurka domin shirya sosai kan wannan ziyarar shugaba Obama.

Yang ya kara da cewa, ana sa ran kasashen biyu za su kara zurfafa hadin kansu da samun daidaituwa a fannoni daban-daban da wasu manyan batutuwan kasa da kasa, da kara mu'amala a tsakanin kasashen da ke Asiya da tekun Pacific, gami da daidaita wasu matsalolin dake shafar kasashen biyu yadda ya kamata, a kokarin kara samun kyawawan sakamako yayin da ake raya dangantaka ta sabon salo a tsakanin Sin da Amurka, ta yadda za su taka muhimmiyarwa rawa wajen samun zaman lafiya da na karko da kuma wadata a kasa da kasa da na shiyya-shiyya.

A nata bangare, Madam Susan Rice ta furta cewa, Amurka na dukufa kan raya dangantaka ta sabon salo a tsakanin kasashen biyu, tare kuma da tinkarar kalubalolin da ke gaban kasa da kasa baki daya. Shugaba Obama na nuna kyakkawar fata ga wannan ziyararsa a kasar Sin da kuma ganawar da zai yi da shugaba Xi Jinping. Dadin dadawa, a cewarta, Amurka na fatan kara hadin gwiwa da kasar Sin domin tabbatar da samun nasarar wannan ziyara, kana da sa kaimi wajen samun ci gaba a yayin kwarya-kwaryar taro na APEC da za a yi ba da jimawa ba. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China