in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a yi kwarya-kwaryan taron kolin APEC karo na 22 a nan birnin Beijing
2014-10-20 20:03:06 cri

A yau Litinin ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya sanar da cewa, za a yi kwarya-kwaryan taron kolin kungiyar hadin kai tattalin arziki na nahiyar Asiya da yankin tekun Pacific APEC daga ran 10 zuwa 11 ga watan Nuwamba a nan birnin Beijng.

Taron na wannan karo mai taken "kafa dangantakar abokantaka tsakanin kasashen nahiyar Asiya da yankin tekun Pacific", ana saran zai samu halartar shugabanni ko wakilan kungiyar APEC, ciki hadda shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda kuma zai jagoranci taron.

Ban da haka kuma, za a yi taron kolin APEC a fannin masana'antu da ciniki tare da yin shawarwari tsakanin shugabannin APEC da majalisar ba da shawara kan harkokin masana'antu da ciniki daga ran 9 zuwa 10 ga watan Nuwamba mai zuwa a nan birnin Beijing.

Daga cikin shugabanni ko wakilan kungiyar ta APEC da za su halarci taron, hadda shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda zai yi jawabi. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China