Shugaban kasar Sin zai ziyarci kasashen Indonesiya da Malaysia tare da halartar taron APEC
A ranar 29 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, ya sanar da cewa bisa goron gayyatar da shugaban kasar Indonesiya Susilo Bambang Yudhoyono, da takwaransa na kasar Malaysia Tuanku Abdul Halim Muadzam Shah suka gabatar, shugaban kasar Sin zai kai ziyarar aiki kasashen Biyu tun daga ranar 2 zuwa ranar 8 ga watan Octoba mai zuwa.
Baya ga ziyara a wadannan kasashe, shugaba Xi, zai kuma halarci kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin yankunan Asiya, da tekun Fasific wato APEC karo na 21 a tsibirin Bali na kasar Indonesiya.(Bako)