Yau juma'a 7 ga wata, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da shugaban girmamawa na jam'iyyar KMT ta kasar Sin Lian Zhan a birnin Vladivostok na kasar Rasha.
A yayin ganawar da suka yi, mista Hu Jintao ya lura cewa, kawo yanzu, an riga an cimma yawancin burin tabbatar da bunkasuwa a gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan cikin lumana da shugabannin jam'iyyun biyu wato JKS da KMT suka gabatar a shekarar 2005, a dalilin haka, ana iya cewa, hanyar cigaban dangantakar dake tsakanin gabobin biyu da jam'iyyun biyu suka zaba ta yi kyau kuma ta dace da yanayin da ake ciki, saboda haka, makomar cigaban dangantakar dake tsakanin gabobin biyu tana da haske.
A don haka, in ji shugaba Hu Jintao, ya kamata jam'iyyun biyu da bangarorin biyu dake gabobin biyu na mashigin tekun Taiwan su cigaba da kan wannan hanya, ta yadda za su kara inganta da zurfafa yalwatuwar dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata, kana kuma su cimma burin tabbatar da farfadowar babbar al'umnar kasar Sin tare.
Kan wannan batu, Shugaba Hu Jintao ya gabatar da ra'ayoyi uku wadanda suka hada da, na farko, dole ne a nace ga hanyar bunkasa dangantakar dake tsakanin gabobi biyu cikin lumana. Sannan na biyu shi ma dole ne a kara karfafa tushen siyasa domin cimma wannan burin, ganin a cikin 'yan shekarun da suka gabata, bangarorin biyu na gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan sun kafa tushen siyasa iri daya kamar su nuna kiyayya ga 'yancin kan Taiwan da kuma nace ga ra'ayi daya na "kasar Sin daya tak a duniya" da suka cimma a shekarar 1992, duk wadannan sun fi muhimmanci ne yayin da ake gudanar da huldar dake tsakanin gabobin biyu, wato babban yankin kasar Sin da lardin Taiwan. Sai na uku, wanda ya ce, ya kamata a kara mai da hankali kan makomar dangantakar dake tsakanin gabobi biyu yayin da ake fuskantar sauye-sauyen yanayin kasa da kasa tare kuma da kokarin farfadowar al'ummar kasar Sin.
Game da yanayin tattalin arziki da lardin Taiwan ke ciki, mista Hu Jintao yana fatan za a kara karfafa hadin gwiwa mai moriyar juna domin tabbatar da bunkasuwa tare, kana bangarorin biyu za su dakile sabon kalubalen da yanayin tattalin arzikin kasa da kasa ke kawo musu tare, ban da wannan kuma ya nuna cewa, yana son cigaba da yin shawarwarin hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin gabobin biyu bisa manyan tsare-tsaren da aka tsara.
Mista Lian Zhan a nasa bangaren ya bayyana cewa, ra'ayi daya na "kasar Sin daya tak a duniya" da aka cimma a shekarar 1992 shi ne tushe mafi muhimmanci wajen bunkasa dangantakar dake tsakanin gabobi biyu cikin lumana, yana fatan bangarorin biyu za su kara zurfafa zumuncin dake tsakaninsu tare kuma da kara karfafa hadin gwiwa domin ciyar da bunkasuwar dangantaka tsakaninsu cikin lumana yadda ya kamata.(Jamila)