Shugaba Hu ya nuna cewa, a cikin 'yan kwanakin nan, kasar Sin da kasar Japan na cikin wani hali mai tsanani sakamakon batun tsibirin DiaoYu. Ko da yaushe kasar Sin ba ta canja matsayinta kan batnn tsibirin Diaoyu ba. Haka kuma, Shugaba Hu ya jaddada cewa, ko wane matakin da Japan za ta dauka ta ko wace hanya wajen sayen tsibirin Diao Yu haram ne kuma maras amfani, kasar Sin ba za ta yarda da wannan manufa ko kadan ba. Gwamnatin kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan kiyaye ikon mallakar yankunan kasarta. Dole ne kasar Japan ta fahimci tsananin yanayin da ake ciki yanzu, da daina aikata kuskure. Ya kamata ta yi kokari tare da kasar Sin domin ciyar da dangantaka a tsakaninsu zuwa gaba.(Maryam)