in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Hu Jintao ya yi jawabi a yayin taron koli karo na 20 na matakin biyu na kungiyar APEC
2012-09-10 17:41:59 cri
A ran 9 ga wata, an bude kwarya-kwaryar taron koli karo na 20 na mataki na biyu na kungiyar hadin gwiwa a tsakanin kasashen Asiya da na tekun Pacific ta fuskar tattalin arziki watau APEC a birnin Vladivostok ta kasar Rasha, inda shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi jawabi kan yadda za a tabbatar da samun isasshen hatsi da inganta hadin gwiwa ta fuskar kirkire-kirkire.

Game da batun tabbatar da samun isasshen hatsi, shugaba Hu ya jaddada cewa, wannan batu ya shafi zaman rayuwar jama'ar kasa da kasa, da kuma ci gaba da lafiyar bil Adam, don haka ya kamata a kara yawan kudin da ake ware ma aikin noma, don kyautata halin fasahohin noma. Sannan kuma dole ne a inganta muhimman ayyukan more rayuwar jama'a na kasuwar cinikin hatsi, a kokarin kafa tsarin rarraba hatsi a zihiri.

Haka kuma in ji shi, ya kamata a kara zuba kudi kan aikin noma da yin nazari kan fasahohin da abin ya shafa domin ba da tabbaci ga ingancin abinci, kuma dole ne a tabbatar da samun farashin hatsi ba tare da tangarda ba, da kuma daukar matakan da suka dace don samar da abinci ga mutane marasa galihu yadda ya kamata.

A kan batun inganta hadin gwiwa ta fuskar kirkire-kirkire, shugaban na kasar Sin ya nuna cewa, ya kamata a kago sabon muhalli ga aikin kirkire-kirkire, da kara zuba kudi kan aikin nazari, da horar da kwararru masu iya kirkiro sabbin fasahohi da masu rike da fasahohin zamani. Bugu da kari, ya kamata gwamnatocin kasa da kasa su taka rawa wajen samar wa masana'antu dandalin hadin gwiwa kan aikin kirkire-kirkire.

Taron ya bayar da sanarwar shugabanni, kuma daga karshe an sanar da cewa, za a yi kwarya-kwaryar taron koli karo na 21 a kasar Indonesia a shekara mai zuwa.(Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China