in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kira kwarya-kwaryar taron koli na 20 na kungiyar APEC
2012-09-08 17:45:31 cri

An kira kwarya-kwaryar taron koli na kungiyar APEC a ranar 8 ga wata a birnin Vladivostok, hedkwatar jihar Primorsky Krai ta kasar Rasha, inda shugaban kasar Sin Hu Jintao ya ba da wani muhimmin jawabi.

A cikin jawabinsa, Hu ya bayyana cewa, kokarin yin cinikayya da zuba jari cikin 'yanci, da samun dunkulewar tattalin arziki a shiyya-shiyya babban batu ne da ake tattaunawa a kai a cikin kungiyar APEC. Ya kamata a bi ra'ayin cimma burin Bogor da aka gabatar a shekara ta 1994, da kuma sa kaimi ga yunkurin yin cinikayya da zuba jari cikin 'yanci. Haka kuma ya kamata a daidaita dangantaka a tsakanin sabbin batutuwan da za a tattauna a kai da burin Bogor, kasar Sin ta goyi baya kan batun mayar da yadda za a tabbatar da adalcin yarjejeniyar yin cinikayya cikin 'yanci a matsayin muhimmin batun da za a tattauna a kai a bana. Haka zakila, za a sa kaimi ga samar da kayayyakin da suka shafi muhimman halittu cikin 'yanci bisa yin la'akari da bambancin matsayin ci gaba da kasashe membobin kungiyar suka cimma. Bugu da kari kuma, za a karfafa yaduwa da bunkasuwar fasahohin da suka shafi muhallin halittu domin tallafa wa membobi kasashe masu tasowa wajen raya sana'ar muhalli da kyautata kwarewarsu wajen samun dauwamammen ci gaba. Ban da wannan kuma, za a inganta musayar bayanai a tsakaninsu, da neman samun sabon ra'ayi kan batun dunkulewar tattalin arziki na shiyya shiyya, a kokarin kara azama ga aikin raya yankin ciniki maras shinge na shiyyar Asiya da tekun Pacific sannu a hankali bisa ka'idojin bude kofa da kiyaye adalci da hakuri.

Shugaba Hu ya kara da cewa, ko da yaushe kasar Sin ta kan dora muhimmanci kan rawar da kungiyar APEC ke takawa, da kuma hadin gwiwa tare da bangarori daban daban cikin yakini. Kasar Sin na son amfani da kyakkyawar damar shirya kwarya-kwaryar taron koli na kungiyar a shekara ta 2014 wajen inganta hadin gwiwa tare da kasashe membobin kungiyar domin bayar da sabuwar gudummawa ga ci gaba da wadatar shiyyar Asiya da tekun Pacific da ma duniya baki daya, kana da kawo wa jama'a alheri.

An mayar da "hadin kai don samun ci gaba, kirkiro sabbin fasahohi don samun wadata" a matsayin babban jigon wannan taro wanda zai shafe kwanaki biyu ana yinsa, inda shugabanni mahalarta taron za su musanya ra'ayoyinsu kan yin cinikayya da zuba jari cikin 'yanci, samun dunkulewar tattalin arziki a shiyya-shiyya, tabbatar da samun isasshen hatsi, kafa tsarin samar da kayayyaki na matakai daban daban, kana da inganta hadin gwiwa ta fuskar kirkire-kirkire.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China