in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hu Jintao ya isa birnin Vladivostok na kasar Rasha
2012-09-06 17:02:57 cri

Yau Alhamis 6 ga wata da dare, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya isa birnin Vladivostok na kasar Rasha domin halartar taron koli na kungiyar hadin kan yankin Asiya-Pasific karo na 20.

Kungiyar APEC dai tana kunshe da mambobin kasashe 21 ciki har da Sin, Amurka, Rasha da Japan, kuma ta kasance dandalin tattalin arziki mafi muhimmanci a wannan yanki, wanda yawan GDP na mambobin kasashen ya kai kashi 56 bisa dari da dukkan duniya ke samu, kuma yawan kudin da ta samu a fannin ciniki ya kai kashi 48 cikin dari bisa na duk duniya.

A gun taron mai taken "Hadin kai da samun bunkasuwa, da yin kagowa domin samun wadata", za a tattauna kan batun yin ciniki da zuba jari cikin 'yanci da raya yankin bai daya, kara tabbatar da batun samun isashen hatsi, kara yin hadin gwiwa da sauransu.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, Shugaba Hu Jintao zai bayyana matsayin da Sin ta dauka a gun wannan taron kan batun sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin yankin Asiya-Pacific, da kuma matsayin da Sin ta dauka kan wasu muhimman batutuwan da za a tattauna a gun taron kungiyar APEC na wannan shekara, tare da waiwayen sakamakon da APEC ta samu cikin shekaru 20 da suka gabata da hange nesa kan makomar APEC.

A yayin ziyararsa, Shugaba Hu Jintao zai gana da shugabannin mambobin kasashen kungiyar ciki har da shugaban kasar Rasha Władimir Putin.(Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China