A yayin taron na kwanaki biyu, mista Hu tare da sauran shugabannin mambobin kungiyar APEC sun yi musanyar ra'ayoyi kan 'yancin kasasuwanci da zuba jari, dunkulewar yankin tattalin arzikin shiyyar, tsaron abinci, da kuma kafa hanyoyin adanon abinci masu inganci, da ma kuma kyautata huldar bunkasuwa ta kawo sauyi.
Shugaban kasar Sin ya bayyana cewa kasar Sin na son yin amfani da haduwar shugabannin APEC da take fatan shiryawa a kasarta a shekarar 2014 a matsayin wata dama ta kara zurfafa dangantaka tare da sauran mambobin kungiyar APEC da kuma kawo nata babban taimako na samun bunkasuwa, alheri da jin dadin al'ummomin shiyyar yankin Asiya da Pasifik da ma duniya baki daya.
A lokacin da yake tabo magana kan batun 'yancin kasuwanci, zuba jari da kuma dunkulewar tattalin arzikin shiyyar, shugaban kasar Sin ya bayyana cewa an bukaci mambobin kungiyar APEC su da su girmama maradun da aka cimma na Bogor, da mai da hankali gaba kan makomar 'yancin kasuwanci da kawo sauki ga zuba jari da kuma musanyar kasauwanci ta hanyar amfani da yarjejeniyar Bogor a mastsayin tushe.
Hakazalika shugaba Hu Jintao ya bayyana ra'ayin kasar Sin kan hanyoyin da za'a bi wajen bunkasa ci gaban tattalin arzikin shiyyar da na duniya, ta hanyar amfani da matsayin kasar Sin kan maganar tsaron abinci da bunkasuwa ta kawo sauyi. (Maman Ada)