in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Rasha sun yi musayar ra'ayoyi kan hadin gwiwar kasashen biyu
2012-09-07 19:56:53 cri

A ranar 7 ga wannan wata a birnin Vladivostok na kasar Rasha, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan yadda za a zurfafa dangantakar hadin gwiwar kasashen biyu da kuma manyan batutuwan da suka sa ido tare, kuma sun cimma daidaito kan wadannan batutuwa.

Hu Jintao ya nuna cewa, yayin da aka gudanar da taron koli na kungiyar hadin gwiwa ta birnin Shanghai wato SCO a farkon watan Yuni na bana a birnin Beijing, shi da shugaban kasar Rasha Putin sun yi shawarwari, inda suka tabbatar da ka'idojin raya dangantakar kasashen biyu, da makomarsu, da kuma hadin gwiwarsu, ta haka an kara azama ga bunkasuwar dangantakarsu, kana suna fatan bangarorin biyu za su aiwatar da yarjeniyoyin hadin gwiwarsu da suka daddale.

Game da wannan, Hu Jintao ya gabatar da shawarwari 7. Na farko, kamata ya yi a kara samun fahimtar juna, da nuna goyon baya ga juna a fannin siyasa don tabbatar da samun ci gaban dangantakar siyasa a tsakanin kasashen biyu. Na biyu, a kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu a fannonin zuba jari, fasahohin zamani, kirkire-kirkire da dai sauransu, da inganta hadin gwiwarsu a manyan ayyuka da kuma hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu. Na uku, a yi shawarwari kan shirin aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Rasha na shekarar 2013 zuwa ta 2016, da gudanar da shi bisa ka'idoji yadda ya kamata. Na hudu kuma ya ce, a kafa tsarin hadin gwiwar kasashen biyu a fannin tsaro don raya dangantakar sada zumunci a tsakanin sojojinsu. A na biyar, shugaba Hu ya bukaci a kafa tsarin ganawa a tsakanin shugabannin yankunan kasashen biyu. Sannan a na shida, a tattauna kan shirin yin hadin gwiwarsu a fannin al'adu a cikin shekaru 10 masu zuwa, da gudanar da bikin yawon shakatawa a tsakanin kasashen biyu, da kuma sa kaimi ga yin mu'amala a tsakanin matasan kasashen biyu. Sai na karshe, na bakwai, da ya bukaci bangarorin biyu su yi hadin gwiwa kan manyan batutuwan duniya da yankuna, da kiyaye ka'idojin tsarin MDD da kuma ka'idojin raya dangantaka a tsakanin kasa da kasa, da tabbatar da samun adalci a duniya, da kuma sa kaimi ga samun zaman lafiya da na karko a dukkan duniya.

Haka kuma shugaba Hu Jintao ya jaddada cewa, hadin gwiwar makamashi muhimmin aiki ne na Sin da Rasha yayin da suke yin hadin gwiwa, za a yi aikin bisa manyan tsare-tsare a dogon lokaci. Don haka, yana fatan kasashen biyu za su bi ka'idar samun moriyar juna da kuma sa kaimi ga samun sabon ci gaba kan hadin gwiwarsu.

Ban da wannan kuma, a cikin shawarwarin, Hu Jintao ya ce, kasashen Sin da Rasha su ne manyan kasashe a yankin Asiya da tekun Pasific, kana sun kasance muhimman kasashe da suka sa kaimi ga yin hadin gwiwa a yankin. Kasar Sin tana son ci gaba da yin kokari tare da kasar Rasha wajen shimfida zaman lafiya da yin hadin gwiwa cikin adalci a yankin Asiya da tekun Pasific.

A nasa bangaren shugaban Rasha, Vladimir Putin ya bayyana cewa, a karkashin kulawa da shugabannin kasashen biyu suka sa, ana samun babban ci gaba wajen raya dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha. Don haka kasar Rasha tana son yin kokari tare da kasar Sin wajen aiwatar da shirye-shiryen da shugabannin kasashen biyu suka tsara, ta haka za a inganta dangantakar abokantaka da hadin gwiwarsu zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China