Yau Alhamis 6 ga wata, bisa goron gayyata na shugaban kasar Rasha Władimir Putin, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya bar birnin Beijing kuma yana kan hanyar zuwa birnin Vladivostok na kasar Rasha domin halartar kwarya-kwaryan taron koli na kungiyar hadin kan yankin Asiya-Pasific APEC karo na 20.
Za a kira wannan taro daga ran 8 zuwa 9 ga wata bisa taken "Hadin kai da samun bunkasuwa da yin kagowa domin samun wadata". A gun taron za a tattauna kan batun yin ciniki da zuba jari cikin 'yanci da raya yankin bai daya, kara tabbatar da batun samun isashen hastsi, kara yin hadin gwiwa da sauransu. A kwanan baya, hukumomin kasar Sin sun nuna cewa, Sin tana fatan a kara tabbatar da yin cikini da zuba jari cikin 'yanci bisa ka'idar yarjejeniyar Bogor Goals, ta yadda za a tabbatar da raya tattalin arzikin yankin bai daya da kara hadin kai tsakanin mambobin kungiyar APEC. Har ma da tabbatar da kara samun isashen hatsi da harkokin sadarwa na Intanet a wannan shiyya. Tare kuma da tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin yankin Asiya-Pasific yadda ya kamata.(Amina)