Kungiyar WHO ta yi gargadin cewa, yanzu cutar Ebola tana ci gaba da yaduwa a Liberiya, musamman ma a birnin Monrovia. Koda yake ba bu Akwai shaidun da ke cewa, akwai karin masu kamuwa da cutar Ebola a wurinda ba a bayyana ba. Kungiyar WHO ta ce, babu alamar cewa an shawo kan cutar Ebola.
A wannan rana kuma, Anthony Banbury, shugaban tawagar musamman na MDD kan cutar Ebola da Ban Ki-moon ya nada ma ya kai ziyara a Liberiya, domin nazarin hakikaninhakikanan abubuwan da kasar ke bukata wajen shawo kan cutar Ebola.(Fatima)