A ranar Litinin 6 ga wata ne shugaba Barack Obama na kasar Amurka ya ce, cutar Ebola tana kawo illa ga tsaron kasashen duniya. Don haka ya yi kira ga kasashen duniya da su kara hada kansu domin kara karfin yaki da cutar ta Ebola.
A wannan rana da yamma, Obama ya yi taron gaggawa tare da manyan jami'an kiwon lafiya na gwamnatin da kuma masu ba shi shawara kan tsaron kasa dangane da cutar Ebola. A yayin taron manema labaru da aka yi bayan taron, Obama ya bayyana cewa, wasu kasashe ba su yi kokarin da ya dace ba wajen agazawa kasashen Afirka yaki da cutar. Ya yi fatan karin kasashe za su shiga aikin yaki da cutar cikin hanzari, a maimakon kallo kawai.
Har wa yau Obama ya sanar da cewa, ko da yake kusan babu yiwuwar barkewar cutar Ebola a Amurka, amma kasarsa za ta inganta aikin binciken lafiyar fasinjojin da ke tafiye-tafiye ta jiragen sama, a kokarin yin rigakafin yaduwar cutar a Amurka.
Yanzu mutum na farko da Amurka ta tabbatar ya kamu da cutar yana cikin matsanancin hali. (Tasallah)