in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka za ta fara inganta bincike a filayen saukar jiragen sama 5 game da Ebola
2014-10-09 09:44:46 cri

Matafiya daga kasashen dake fama da cutar Ebola za su fuskanci bincike sosai a manyan filayen saukar jiragen sama guda biyar na Amurka, kamar yadda gwamnatin kasar ta sanar a jiyar Laraba 8 ga wata, awanni bayan da wani 'dan kasar Liberiya wanda ya zama mutum na farko da aka gano yana dauke da cutar ya mutu a wani asibiti dake Dallas.

Matafiya daga kasashen Guinea, Liberiya da Saliyo, za'a auna zafin jikinsu, kuma dole ne su amsa tambayoyi game da lafiyarsu da tarihin wuraren da suka ziyarta a baya, in ji cibiyar kula da kuma ba da kariya a kan cututtuka da sashen tsaro na kasa da bangaren shige da fice da ba da kariya a kan iyaka na kasar Amurka suka bayyana cikin wata sanarwa ta hadin gwiwwa.

Filayen saukar jiragen saman dai sun hada da na birnin New York wato JF Kennedy da zai fara nashi binciken tun daga ranar Asabar din nan mai zuwa. Sannan manyan filayen saukar jiragen sama na Washington-Dulles, Newark, Chicago-O'Hare, da Atlanta za su fara nasu binciken a mako mai zuwa, in ji sanarwar.

Yin wannan ingantaccecn binciken a wuraren shigowa kasar na manyan filayen saukar jiragen saman guda biyar, Amurka za ta iya tantance kusan kashi 94 cikin 100 na matafiya daga kasashen Guinea, Liberiya da Saliyo, kasashe uku daga yammacin Afrika da wannan cuta ta Ebola ta yi kamari, in ji sanarwar.

Sabon matakin da aka sanar ya biyo bayan mutuwar Thomas Eric Duncan wanda aka fara gano cutar Ebola na farko a tare da shi a Amurka awannin da suka gabata. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China