Sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon ya sanar a ranar Laraba da nada jami'an daidaita matsaloli a kasar Guinea, Liberiya da Saliyo bisa tsarin ayyukan gaggawa na kungiyar domin yaki da annobar cutar Ebola a yammacin Afrika.
A cikin wata sanarwa, kakakin mista Ban Ki-moon ya nuna cewa, Marcel Rudasingwa na kasar Rwanda, an nada shi jami'in daidaita matsala a Guinea, Peter Jan Graff na kasar Holand a kasar Liberiya, sai kuma Amadou Kamara, 'dan kasar Amurka a Saliyo.
A cewar sanarwar, wadannan nade-nade na cikin shirin kafa tawagar MDD domin aikin gaggawa kan yaki da Ebola (MINUAUCE). Wadannan jami'ai uku za su aiki tare da gwamnatocin kasashen uku domin tabbatar da matakin kasa da kasa na gaggawa, kuma mai nagarta game da annobar Ebola a cikin wadannan kasashe uku.
Guinea, Liberiya da Saliyo sun kasance kasashen yammacin Afrika uku da suka fi fama da cutar Ebola.
Ta wani bangare, shugabar tawagar MDD a Liberiya (MINUL), Karin Landgren ta sanar a ranar Laraba cewa, wani ma'aikacin waje na tawagar, an yi gwajin yana dauke da cutar Ebola. Wannan shi ne mutum na biyu da ya kamu da cutar a cikin tawagar. Wani ma'aikacin kasar na MINUL ya rasu a ranar 25 ga watan Satumba bayan ya kamu da cutar. Madam Landgren ta bayyana cewa, MINUL ta dauki dukkan matakan da suka dace domin kaucewa sake bullar cutar a cikin tawagar, ko a wajenta. (Maman Ada)