in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka za ta iya tura sojoji zuwa 4000 a Liberiya domin daidaita matsalar cutar Ebola
2014-10-04 16:55:58 cri
Fadar Pentagone ta bayyana a ranar Jumma'a cewa tana shirin tura sojoji 4000 a Liberiya bisa tsarin da ya shafi shirin bada taimako wajen yaki da annobar cutar Ebola, tare da nuna cewa adadin gaskiya ka iyar canjawa.

Sakataren tsaron Amurka, Chuck Hagel ya amince da yiyuwar tura sojoji 4000 a Liberiya in ji jam'in dake kula da hulda da 'yan jarida na Pentagone, mista John Kirby a yayin wani taron manema labarai. Sai dai ya cewarsa akwai yiyuwar tura sojoji, kuma wannan ba ya nufin ba za'a cimma adadin ba. Yawan tawagar ya kai kusan mutane 1000, wanda ya karu bisa ga wanda shugaba Barack Obama ya alkawarta da farko, an bayyana hakan bayan an gano mutum na farko da ya kamu da cutar Ebola a kasar Amurka a makon da ya gabata, lamarin da ya sanya hukumomin kiwon lafiya na kasar cikin shirin ko ta kwana.

A halin yanzu, akwai sojojin Amurka 205 a Liberiya kana wasu 26 a Senegal, makwabciyar kasarta in jin Pentagone.

A tsawon sa'o'i 36 na baya bayan nan, dakunan bincike na biyu na gwajin cutar Ebola dake karkashin kulawar ma'aikatan cibiyar binciken kiwon lafiya ta rundunar sojojin ruwan Amurka sun fara aiki gadan gadan, kana sun tanadi karfi da kwarewar yin bincike kan kimanin nau'o'in cuta 100 a kowace rana in ji mista Kirby. Haka kuma ayyukan gina wasu cibiyoyin bincike ga sauran masu fama da cutar Ebola zasu fara ranar yau kuma su kare nan da karshen wata in ji wannan jami'in.

Mista Kirby ya yi alkawarin himmatuwa wajen kara gaggauta ayyuka a Liberiya da ma kara yawan sojoji.

Rundunar sojojin Amurka ta bayyana cewa ta dauki niyyar tura sojoji 3200, da zasu samar da tallafin kiwon lafiya da na kayayyaki, kana kuma zasu tabbatar da tsaro a yankunan da suka fi fama da cutar Ebola. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China