Darekta janar ta hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO), dokta Margaret Chan, ta bayyana a ranar Litinin cewa, a duk tsawon rayuwar aikinta, ba ta taba ganin matsalar kiwon lafiya irin wannan ba ta annobar cutar Ebola, dake bayyana karara, a cewarta, haduran dake janyo bambance bambancen dake karuwa a duniya.
A cikin tsawon rayuwar aikina a bangaren kiwon lafiya, ban taba ganin wata matsalar kiwon lafiya irin wannan ba dake kawo fargaba da tsoro, nesa da kasashen da cutar ta fi kamari, in ji madam Chan, a cikin wani jawabin da babban darektan ofishinta a WHO, Ian Smith ya karanta a yayin zaman taron kwamitin shiyya na hukumar a Manila na kasar Philippines.
A cewar shugabar WHO, annobar na bayyana a fili haduran bambance bambancen tattalin arziki da na jama'a dake karuwa a duniya. Masu arziki na samun aikin jinya mafi inganci, sannan ana barin matalauta na mutuwa.
Haka kuma madam Chan, ta nuna cewa, Ebola ta bayyana ne yau da kusan shekaru 40 da suka gabata, amma ba'a kirkiro wata allurarta tun lokacin. Domin Ebola, an killace ta, bisa tarihi, kuma a shiyyar kasashen Afrika masu talauci.
A karshe, a cewarta, duniya ba ta shirya da kyau ba domin fuskantar duk wata matsalar kiwon lafiya da gaggawa, ta karko da mai hadarin gaske. (Maman Ada)