Kwamitin kula da tsari da kasafin kudi na MDD a ranar Talatan nan ya amince da ware kudi har dala miliyan 49.9 domin kafa sabon ofishin da zai kula da duk wassu bukatu da suka jibanci tallafi ga ayyukan kariya daga cutar Ebola cikin gaggawa UNMEER.
Kafa wannan ofishi shi ne na farko a cikin kokarin da majalissar ke yi na hana yaduwar cutar a duniya baki daya, abin da za'a cigaba da yi ta hanyar gabatar da ayyuka da matakai daga dukkan fannoni kamar yadda shugaban babban taron majalissar na wannan karon Sam Kutesa ya shaida wa wani taron majalissar karo na biyu.
A lokacin ganawar farko ta kwamitin na biyar a ranar Jumma'ar nan Susana Malcorra, babban jami'i na magatakardar majalissar ya gabatar da takardun bayanin game da bukatar kudi dalar Amurka miliyan 49.9 don ayyukan har karshen shekara.
Sakamakon amincewar kwamitin na wannan adadin kudade, Mr Kutesa ya ce, hakan na aika sako mai karfi dake bayyana aniyarsa ta ganin ya kula da bukatu na gaggawa a duniya baki daya, don haka ya yi kira da a samar da aminci a tsakanin mambobi, sannan a gabatar da ayyukan yadda ya kamata a cikin lokaci. (Fatimah)