Kwamitin sulhu na MDD ya bukaci mambobin kasashe da su ci gaba da huldar cinikayya da sufuri da kasashen da cutar Ebola ta fi shafi, ta yadda za su hanzarta cin gajiyar tallafin albarkatun da aka samar musu.
A dangane da wannan batu ne kwamitin ya bukaci kamfanonin jiragen sama da na ruwa da su amsa kiran majalisar yayin da suke daukar matakan da suka shafi kariya.
Bugu da kari, kwamitin sulhun ya bayyana rashin jin dadinsa game da haramcin cinikayya da zirga-zirga da aka sanya wa kasashen da wannan matsala ta Ebola ta shafa, da kuma yadda ake nuna wa 'yan asalin kasashen Guinea, Liberia da Saliyo wariya da tsangwama.
Daga karshe, kwamitin ya zayyana sunayen wasu albarkatu a cikin sanarwar da ya bayar da ya ce, ana matukar bukatar su a wadannan kasashe, da suka hada da dakunan bincike na tafi da gidanka, asibitocin kula da wadanda suka kamu da cutar, magunguna da na'urorin gwajin marasa lafiya, da kuma kayayyakin kariya daga cutar. (Ibrahim)