A yayin wani taron da aka yi a bainar jama'a kan cutar Ebola da kwamitin sulhu na MDD ya shirya a ran 14 ga wata, Mr. Banbury ya yi wa kwamitin sulhun bayani ta hoton bidiyo, inda ya ce, hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa WHO ta gabatar da matakan hana yaduwar annobar, wato da farko dai, kebe da kumasa-ido kan wadanda suka yi cudanya da wadanda suka kamu da cutar, sannan sa ido kan wadanda suka kamu da cutar, bugu da kari, dole ne a binne gawawwakin wadanda suka kamu da cutar yadda ya kamata. Daga karshe a samar da bayanai kan yadda za a iya magance kamuwa da cutar ga jama'a.
Mr. Banbury ya jaddada cewa, wadannan matakai sun kasance matakai masu sarkakiya a wuraren da ake fama da cutar. Ya ce, idan aka gamu da matsala a daya daga cikin wadannan matakai 4, dukkan kokarin shawo kan cutar zai bi ruwa ke nan
Mr. Banbury ya kara da cewa, bisa kididdigar da hukumar WHO ta yi, ya zuwa ran 1 ga watan Disamban bana, ana bukatar gadajen kwantar da marasa lafiya dubu 7 a asibitoci, amma bisa aikin da ake yi yanzu, za a iya samar da gadaje 4300 ne kawai, kuma babu isassun likitoci. Bugu da kari, ana bukatar sabbin dakunan gwaji 15. Ya kuma ce kamata ya yi a kara kungiyoyin ma'aikata na yin aikin binne gawawwakin wadanda suka kamu da cutar daga guda 50 da ake da su a halin yanzu zuwa dari 5. Sannan, dole ne a samar da isassun na'urori da kayayyakin shawo kan cutar. (Sanusi Chen)