in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta tabbatar wa 'yan kasar ta kudurin ta na hana yaduwar cutar Ebola a kasar
2014-10-04 16:28:17 cri
Jami'an lafiya na kasar Amurka sun sake nanata wa Amurkawa cewa, kasar ta Amurka na da ingantattun kayayyakin kiwon lafyar da za su dakatar da bullor cutar Ebola a kasar .

Mataimakiyar mai baiwa shugaba Obama shawara kan harkokin tsaro Lisa Monaco ce ta bayyana hakan yayin da ta ke jawabi a fadar white house game da matakin da Amurka ke dauka bayan da aka samu rahoton bullar cutar Ebola a karon farko a kasar,bayan wani dan kasar Liberian nan da aka tabbatar a asibitin Dallas ranar Talata ya kamu da cutar.

Shi dai Thomas Eric Duncan, dan kasar Liberia ya iso Dallas ne ranar 20 ga watan Satumba,inda bayan wasu kwanaki ya fara nuna alamun yana dauke da cutar Ebola,sannan ya je asibiti a ranar 26 watan Satumba wanda daga bisani aka sallame shi bayan an ba shi maganin kashe kwayoyin cuta.

Bayan ya koma asibitin a ranar 28 ga watan Satumba sai aka tabbatar a ranar 30 ga watan na Satumba cewa, shi ne mutum na farko da aka gano yana dauke da cutar ta Ebola a cikin kasar ta Amurka, ko da ya ke yanayin da ya ke ciki bai tsananta ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China