Anthony Banbury, shugaban tawagar ba da taimakon gaggawa a kan Ebola na MDD ya bayyana hakan a lokacin wani zaman tattaunawa a cibiyar majalissar dake birnin New York.
Bunbury ya jaddada cewar, annobar Ebola ta haifar da wani babban kalubale ga kasashen Liberiya, Saliyo da Guinea, musamman yadda yanayin zamantakewa da harkokin al'adu yake kawo cikas ga saurin dakile ta saboda har yanzu wassu mutane ba su yarda da cewar akwai shi ba.
Jami'in na MDD ya yi kira ga matakin gaggawa daga sauran kasashen duniya tun da tawagarsa ba za ta iya yaki da wannan annoba ba ita kadai, dole sai sauran kasashe sun ba da gudunmuwa da suka hada da karfafa ayyukan wuraren ba da jinya, da dakunan gwajin kwayoyin cutar, sannan a hada da taimakon kudin agaji, har ma a shirya wani amintaccen wuri domin ba da jinya ga wadanda suka kamu da cutar, ko kuma inda za'a kebe ma'aikatan kiwon lafiya dake ba da taimako ga masu dauke da cutar.
Kamar yadda kididdigar hukumar kiwon lafiya ta MDD ta fitar a ranar Jumma'ar nan 10 ga wata, fiye da mutane 8,000 ake ganin ko kyautata zaton sun kamu da cutar ta Ebola kuma ya zuwa yanzu, fiye da mutane 4,000 daga cikin su sun mutu tun daga lokacin da annobar ta barke a watan Maris. (Fatimah)