Rukunin masu bincike kwayoyin cutar Ebola na cibiyar yin rigakafi da shawon kan cututuka na kasar Sin ya bayyana cewa, ya zuwa karfe shida na yammacin ranar Alhamis 2 ga wata, ya gudanar da bincike kan samfurin kwayoyin cutar guda 121, inda ya tabbatar da cewa 62 daga cikinsu suna dauke da kwayoyin cutar.
A cikin wadannan samfuri 121, yawancinsu sun fito ne daga wuraren dake yammacin Freetown, wuraren da suke fi fama da cutar. An ba da labari cewa, tun lokacin da rukunin suka karbi wadannan samfuri daga ran 28 ga watan Satumba, yawan samfurin da rukunin suka gudanar da bincike a kan su da kuma wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar sun wuce rabin yawan samfurin da aka yi bincike a kan su a yammacin kasar.
Shugaban rukunin Qian Jun ya yi bayanin cewa, su kan yi aiki na fiye da sa'o'i 12 a ko wace rana, kuma sun yi amfani da nu'urorin da Sin ta kirkiro domin yin bincike da zummar tabbatar da sakamakon bincike. Mr Qian ya ce, wannan rukuni bai taba yin kuskure a bincikensa ba.
An ba da labari cewa, wannan rukuni mai kunshe da ma'aikatan jiyya 59 daga cibiyar yin rigakafi da shawo kan cututuka ta kasar Sin ya isa Freetown ne a safiyar ran 17 ga watan Satumba. (Amina)