A wannan rana kuma, likitocin Sin sun ba da jiyya ga sun karbi mutane 7 da suka ake zaton sun kamu da cutar Ebola .
Wannan rukuni yana kunshe da likitoci 30, kuma babban aikinsu shi ne tabbatar da aikin cibiyar kan wadanda suka kamu da cutar Ebola. Bayan da rukunin ya isa Saliyo a ranar 17 ga watan Satumba, ya kyautata gyara asibitin zuwa wurin dake iya ba da jiyya ga wadanda suka kamu da cutar dake yaduwa cikin sauri.(Fatima)