Ministan lafiya na kasar Mali Ousmane Kone ya yaba wa kasar Sin game da kokarinta na yaki da cutar Ebola a kasar, Kone yana magana ne a wajen bikin karban na'urorin zamani na ma'aunin zafin jiki guda 185 da gwamnatin kasar Sin ta ba da gudunmuwa ta hannun jakadanta a Mali Cao Zhongming.
Ministan ya ce, wannan gudunmuwa wata alama ce dake nuna yadda a ko da yaushe kasar Sin ke ba da taimakonta da hadin gwiwwa da kasar Mali, sannan ya tabbata da cewar, wadannan na'urori, za'a yi amfani da su yadda ya kamata wajen yaki da cutar.
Ya ce, kamar kullum ya gamsu kwarai da wannan gudunmuwa da kuma sanarwar wani a nan gaba. Wannan taimakon da gwamnatin kasar Sin ta bayar wanda ya zo bayan wata gudumuwa da tun da fari wata kamfanin kasar Sin ta bayar ta kwatankwacin sefa miliyan 40 zai taimaka matuka wajen kokarin hana shigowar cutar ta Ebola cikin kasar.
A cikin bayaninsa, jakadan kasar Sin a Malin ya ce, baya ga wannan gudumuwa da yake a kwatankwacin sefa miliyan 9 ko kuma dalar Amurka 17,600, Sin nan gaba kadan za ta kara wasu kayayyakin na kwatankwacin sefa miliyan 400.
Mr. Cao ya kara da cewa, yarjejeniyar hakan ta biyo bayan alkawarin da gwamnatin kasar Sin ta yi ne lokacin ganawar tsakanin shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita da firaministan Sin Li Keqiang lokacin taron sabbin shugabanni na tattalin arzikin duniya a shekara ta 2014, wato taron Davos na lokacin zafi da aka yi a birnin Tianjin daga ranar 10 zuwa 12 ga watan Satumba. (Fatimah)