in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar Liberia ta yaba wa taimakon kasar Sin na yaki da cutar Ebola
2014-09-25 20:51:02 cri
Ranar Alhamis 24 ga wata, a birnin Monrovia, hedkwatar kasar Liberia, an yi bikin sa hannu kan takardar ba da tallafi da kasar Sin take yi wajen yaki da cutar Ebola a Liberia.

A cikin jawabinta a yayin bikin, madam Ellen Johnson-Sirleaf, shugabar kasar ta yaba wa sabon tallafin da kasar Sin ta bayar wajen yaki da cutar. Ta kara da cewa, tallafawin ya sake nuna cewa, har kullum kasar Sin aminiya ce ta gaskiya ga kasarta da ma Afirka baki daya. A daidai lokacin da kasarta ke matukar bukatar kudi da kayayyaki, kasar Sin ta sake ba da taimakon da ya agaza wa Liberia sosai, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen farfado da tattalin arzikin kasarta da sake gina kasar. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China