in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta samu nasarar binciken sigar kwayoyin halittan Ebola a karon farko
2014-09-26 13:25:16 cri

Kwararrun masana daga kasar Sin sun sami nasarar gwajin kwayoyin halitta na Ebola a karon farko, a asibitin hadin gwiwa na kawance tsakanin Saliyo da Sin, wanda ke kilomita 30 daga babban birnin kasar Freetown.

Shugaban ofishin gwaji da ya zo daga cibiyar rigakafi da shawo kan cututtuka ta kasar Sin Qian Jun ya ce, a jiya Laraba ne kasar Sin ta kai ga wannan nasara.

Gwajin da aka yi har rukuni biyar an samo kwayoyin halittu ne daga wani ofishin binciken cututtuka na Afrika ta Kudu wanda ke Lakka a Saliyo.

Binciken da kwararru daga kasar Sin suka yi ya nuna cewar, rukunna hudu da aka auna suna da cutar Ebola a cikin su, to amma rukuni daya an gano ba ya dauke da cutar ta Ebola.

Qian ya ce, kwararrun na Sin suna gudanar da wani bincike domin tabbatar da bayanin gwajin da aka yi na kwayoyin halitta na Ebola, kuma aka gano sakamakon binciken ya zo daidai da na farko.

Wannan shi ne karo na farko da wata tawagar binciken cututtuka ta kasar Sin ta yi gwajin kwayar cutar Ebola, kuma ta samu nasara, binciken da ta yi ya zo daidai da wanda aka kara yi daga baya, don a tabbatar da sakamakon bayanan farko, wannan ya sa nasarar ta kai dari bisa dari a bisa binciken kwayoyin halitta na Ebola.

Wannan ya nuna ke nan na'urorin bincike na kasar Sin na binciken cutar wanda kasar Sin ta kera da kanta suna aiki yadda ya kamata, kuma hanyoyin bincike da ta dauka suna bisa hanya. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China