in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jirgin saman Nigeria zai maido da jigila zuwa Gambia bayan dakatar da  jigilar sakamakon Ebola
2014-09-30 14:38:50 cri

Babban jirgin hada-hada na Nigeria Arik Air zai maido da jigilar jama'a zuwa Banjul, babban birnin kasar Gambia, daga ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa bayan da aka samu tsaiko a sakamakon barkewar Cutar Ebola.

Babban manajan gudanarwa na Arik Air, Chris Ndulue ya shaidawa 'yan jarida a birnin ikko, babban birnin hada-hadar kasuwanci ta Nigeria cewar, tsaron lafiyar fasinjoji da ma'aikatan jiragen saman shi ne muradin jirgin saman na Arik Air, kuma hakan shi ya sa jirgin saman zai ci gaba da aiki kafada da kafada da hukumomin lafiya na cikin gidan Nigeria, da kuma na kasashen duniya, domin kariyar lafiya da jin dadin fasinjoji.

Jirgin na Arik Air zai tafiyar da jigilar jiragensa sau ukku a sati, daga birnin Lagos da Abuja zuwa Banjiul a Laraba da Jumma'a da kuma Lahadi, inda za'a dinga yada zango a Accra ta kasar Ghana. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China