in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin samarwa kasar Najeriya kayayyakin magance cutar Ebola
2014-09-30 20:58:28 cri

An gudanar da bikin musayar takardu tsakanin Sin da Najeriya a talatan nan 30 ga wannan wata a kwamitin tsai da shirye-shiryen kasar Najeriya., takardun da suka shafi kayayyakin magance cutar Ebola da kasar Sin ta samar wa kasar ta Nijeriya. Jakadan kasar Sin dake Najeriya Mr. Gu Xiaojie, karamin jakada mai kula da harkar ciniki Zhou Shanqing, mataimakin shugaban kwamitin Abubakar O.Sulaiman da dai sauran shugabanni sun halarci bikin.

A jawabinsa Jakada Gu ya bayyana cewa, a cikin watanni biyu da suka gabata, Najeriya ta samu ci gaba mai kyau wajen tinkarar cutar Ebola, sai dai duk da haka, tana fuskantar kalubale. Ya jaddada cewa, yanzu cutar Ebola ba kawai barazanace ga yammacin Afrika ba, hatta ma kalubale ne ga harkar kiwon lafiya a dukkan fadin duniya, don haka gwamnati da jama'ar Sin za su marawa Najeriya baya domin hadin gwiwa da ita ta fuskar tinkarar cutar.

A nashi bangare, mataimakin shugaban kwamitin Malam Sulaiman a cikin jawabinsa, ya gode bisa ga taimakon da Sin take bayarwa a daidai wannan lokaci, kuma ya bayyana imani kan cimma nasarar yaki da cutar. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China