Kakakin MDD Stephane Dujarric ya shaidawa manema labarai a yayin wani taron 'yan jarida na kulli yaumin cewar, Alkaluman kididddiga na Hukumar Lafiya ta duniya-WHO na nuni da cewar yawan masu dauke da cutar Ebola a yammacin Afrrica ya kai adadin dubu7,178, kuma daga cikin wannan adadi mutane dubu3,338 sun mutu a sakamakon cutar.
Dujarric ya ce hukumar lafiya ta duniya ta yi amfani da bayanan da ta samu daga ma'aikatun kiwon lafiya na kasashen Guinea, Liberia da Saliyo.
Ya ci gaba da cewar rahoton ya nuna hauhawar annobar Ebola a Saliyo da kuma kusan ace haka lamarin yake a kasar Liberia, amma kuma wani abin mamaki, idan aka kwatanta da Guinea sai a ga ita kasar ta Guinea da alamu ta samu nasarar dakatar da yaduwar cutar ko da yake kamar yadda ya ce abin yana iya canzawa saboda yanayin yaduwar Ebola, wani abu ne da ka iya canzawa a kowane lokaci. (suwaiba)