in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mauritania ta yi kiran samar da allurar rigakafin Ebola a Afrika ta yamma
2014-09-25 14:18:29 cri

Shugaban kasar Mauritania Mohammed Ould Abduel Aziz ya yi kira a kan kasashen duniya da su kara kaimin kokari domin samar da allurar rigakafin cutar Ebola, domin yaki da cutar tare da dakusar da yaduwar cutar a yankin Afrika ta yamma.

Shugaban kasar ta Mauritania, wanda ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi a babban dandalin taron shekara shekara na MDD ya ce, bazuwar cutar a cikin 'dan kankanin lokaci wani gagarumin kalubale ne, saboda da haka sai ya bukaci shugabanni na duniya da su kara karfin jarin da suke zubawa, a fannin kimiyya da bincike na cuce-cuce tare da taimakawa kasashen da cutar ta yi kamari.

Babban sakatare na MDD Ban Ki-moon ya yi shela a wurin taron cewar, zai kira wani taron gaggawa na shugabannin kasashen duniya a cikin wannan mako, domin tattaunawa a kan cutar ta Ebola, wacce wani sabon bincike ya gano cewar, yawan wadanda suka kamu da cutar zai karu idan ba a dauki matakin gaggawa na dakusar da bazuwar cutar ba.

Alkaluman kididdiga daga kasashen Saliyo, Guinea da Liberia inda cutar Ebola ta yi kamari, da aka gabatar ga MDD sun nuna cewar, kawo ya zuwa yanzu, fiye da mutane 5,800 suka kamu da cutar, kuma fiye da wasu mutanen 2,800 suka mutu a sakamakon cutar mai saurin kisan bil'adama. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China