Kasar Sin ta baiwa kasar Ghana kayayyakin dakile cutar Ebola, da darajarsu ta kai dalar Amurka dubu 833, domin taimaka wa kasar tunkarar barkewar cutar Ebola, wacce ta haifar da mutuwar mutane dubu 3 a kasashen Afrika.
A yayin da yake mika kayayyakin ga kasar Ghana, jakadan kasar Sin a Ghana, Sun Baohong ya gabatar da kira a kan kasashen duniya da su hada karfi wuri guda domin murkushe annobar Ebola, wacce ta bazu a Afrika ta yamma, saboda kamar yadda ya ce, yadda cutar ta yadu a halin da ake ciki, dole ne kasashen waje su hada kansu waje guda domin tunkarar wannan kalubalen.
Jakadan kasar Sin a Ghana ya kara jaddada goyon bayan Sin ga hukumar lafiya ta duniya da kuma MDD, a kokarin da suke yi na samar da kudade da kayayyakin aiki na yin gumuzu da cutar Ebola mai saurin kisan bil'adama.
Hakazalika kasar ta Sin bayan tallafin da ta baiwa Ghana, gwamnatin kasar ta kuma bayar da gudumuwar kudin dalar Amurka miliyan guda, da abinci wanda kimar su ta kai dalar Amurka miliyan 2, da kuma gungun kwararrun likitoci na yaki da cutar Ebola ga ko wace kasa da cutar Ebola ta fi kamari, wato Saliyo, Liberia da Guinea.
A kasar Saliyo, Sin ta kuma kafa wata cibiyar bincike da gudanar da gwajin cutar Ebola da wata cibiyar ta tafi da gidanka da kuma wata na'urar auna cutar da ba da kariya ga jikin jama'a.
Kuma Sin ta baiwa Nigeria kyautar kayayyakin dakusar da yaduwar cutar Ebola da kayayyakin agaji, wadanda darajarsu ta kai Renminbi yuan miliyan 10. Ban da haka, kasar Sin ta bai wa kasashen Mali, Benin, Guinea-Bissau da kuma jamhuriyar damokradiyyar Congo kyautar kayayyakin agaji wadda kowanensu darajarsu ta kai yuan miliyan 5.
Kasar Sin ta kuma bai wa kungiyar tarayyar Afrika AU da hukumar lafiya ta duniya WHO dalar Amurka miliyan 2 domin taimaka musu a kokarin da suke yi na daura damara mai karfi domin dakile annobar Ebola. (Suwaiba)