in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Ghana ya ce, Ebola matsala ce da ta shafi daukacin duniya
2014-09-26 10:55:20 cri

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama, wanda kuma shi ne ke rike da akalar shugabancin kungiyar tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma ECOWAS ya ce, cutar Ebola, ba wai ta tsaya ba ne a Afrika ta yamma kawai, matsala ce da ta shafi illahirin duniya baki daya.

Shugaban kasar ta Ghana, wanda ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi a dandalin babban taro na MDD, ya kuma jinjinawa magatakardan MDD, Ban Ki-moon da kuma kwamitin tsaro na MDD, saboda gagarumar guddumuwar da suka ba da wajen kafa wani bangare na MDD, UNMEER, mai zaman shirin ko ta kwana, domin yaki da cutar Ebola a cikin gaggawa.

Mahama ya kuma bayyana a taron na MDD, sakamakon ziyarar da ya kai kasashen Guinea, Saliyo da Liberia, inda cutar Ebola mai saurin kashe bil'adama ta yi kamari, a inda ya ce, cutar Ebola ba ta la'akari da shingen kan iyakoki na kasashen duniya ba. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China