A cikin sanarwar, WHO ta yi kashedi cewa, yanzu cutar Ebola tana ci gaba da yaduwa, kuma an samu sabbin mutane 6 da aka tabbatar sun kamu da cutar Ebola a yankin kan iyakar kasa na kasar Liberia dake dab da kasar Cote d'Ivoire. Kana ana gano bullar cutar a sabon yankin kasar Guinea.
Tawagar aiki ta musamman ta kungiyar AU mai kula da harkokin tinkarar cutar Ebola ta tashi zuwa kasar Liberia a ranar 18 ga wata, kuma sauran tawagogi biyu sun shirya tashi zuwa kasar Saliyo da ta Guinea a ranar 5 ga watan Oktoba da kuma karshen watan Oktoba.
Ban da wannan kuma, a ranar 26 ga wata majalisar gudanarwar asusun ba da lamuni na duniya ta amince da samar da kudaden gudummawa dalar Amurka miliyan 130 ga kasashe 3 na yammacin Afirka mafi fama da cutar Ebola. (Zainab)