Maharan dai sun abkawa garin na Gwoza mai nisan kilomita 135 daga Maiduguri babban birnin jihar ta Borno wanda kuma ke kan iyaka da kasar Kamaru su ka rika harbin kan mai uwa da wabi,inji wata majiyar sojin kasar. Jonas Mark wani mazaunin garin da ya sha da kyar ya bada labarain cewa a lokacin harin an cinna ma mujami'u 2 wuta, da ofishin karamar hukumar,shaguna da gidaje har ma da caji ofis din 'yan sanda kafin jami'an tsaro su kawo dauki.
A wani labarin kuma mutane 20 suka rasa rayukan su da suka hada da wassu mayaka 10 a wani hari da ake zargin 'yan kungiyar boko haram ce ta kai a kauyen Zigague dake arewacin kasar Kamaru kamar yadda wani jami'in soji ya sheda ma kamfanin dillancin labarai na Xinhua.
Kanar Didier Badjeck shugaban sashin sadarwa na ma'aikatan tsaron kasar ya ce maharan sai da tun da farko suka yi arangama da dakarun sojin Kamaru.Ya yi bayanin cewa harin da suka kai na huce haushi ne da suka afkama wata motar safa mai dauke da fasinjoji wanda kuma nan take suka kashe mutane 10 cikin har da wani sojan ko ta kwana na kasar.(Fatimah Jibril)