in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya zata zuba kudi dala miliyan 500 a bangaren albarkatun mai
2014-07-25 20:41:17 cri
A kalla dala miliyan 500 ne za a zuba a ayyukan daban daban da suka jibanci albarkatun mai da iskar gas a cikin 'yan shekaru masu zuwa,inji Ministan albarkatun mai ta Najeriya Diezani Alison Madueke.

Da take Magana a lokacin wata ziyarar a hukumar tattali da sa ido na kasar dake garin Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa mai arzikin man fetur a ranar alhamis din nan,Madam Diezani Madueke tayi bayanin cewa lokacin wannan aiki za'a samar da guraben ayyukan yi har 71,000.

Ministan ta sheda ma wadanda ke wajen a lokacin ziyarar cewa za a saka fiye da kudi daka miliyan 200 a ayyukan da suka jibanci bututun mai da za'a jawo a yanki Polaku dake cikin jihar. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China