An dai samu bayanan hakan ne daga wani asibiti mai zaman kanshi a jihar inji mai bada shawara na musamman ma gwamnana jihar kan harkokin kiwon lafiya,Yewande Adeshina lokacin da take bayani ga manema labarai.
A cewar Madam Adeshina, yanayin jikin mara lafiyan ya nuna cuta ta kama shi sosai,abin da yasa nan take wuraren kula da kiwon lafiya a jihar suka fitar da sabon tsari na koyar da yadda mutane zasu kula da lafiyar su domin guje ma kamuwa da cutar da kuma kariya ga sauran jama'a. (Fatimah Jibril)