in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata Nas data duba mai dauke da cutar Ebola ta mutu a Ikkon Najeriya
2014-08-06 20:32:14 cri
Wata Nas wadda ta yi jinyar mai dauke da cutar Ebola a wani asibiti mai zaman kanshi a jihar Ikkon Tarayyar Najeriya ta mutu,kamar yadda Ministan kiwon lafiyar kasar Onyebuchi Chukwu ya tabbatar ma manema labarai a laraban nan.

A wani labarin kuma mutane 8 ake zarginsu da kamuwa da cutar har ila yau a jihar Ikkon dake kudu maso yammacin Najeriya,su dai wadannan mutanen dukkan su sunyi hulda da Patrick Sawyer dan Asalin kasar Liberiya mai dauke da cutar da ya shigo kasar ya kuma mutu a wani asibitin dake jihar Ikkon kamar yadda kwamishinan kiwon lafiyar jihar Jide Idris ya tabbatar ma manema labarai a Ikeja babban birnin jihar.

A cewar Mr Idris wadansu mutane daban su 6 da suma suka yi hulda da wannan mammacin an masu bincike sai dai ba a ga alamar cutar a tare da su ba a don haka ya tabbatar da cewar gwamnatin jihar ta tsaurara matakan da ya kamata domin binciko duk wadanda suka yi hulda da wannan dan Liberiyan kamin mutuwar sa. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China