Ministan wanda ya bayyana hakan jiya Asabar a jihar Legas, ya kara da cewa yanzu haka matar wadda likita ce, ta kuma kamu da cutar bayan da ta kula da dan kasar Laberiyar nan da ya shigar da cutar Najeriya, na da ikon gudanar da harkokin ta na yau da kullum kamar yadda ta saba kafin ta kamu da cutar.
A cewar ministan lafiyar akwai karin wasu mutum 5 da alamu ke nuna su na daf da samun waraka. A daya bangaren kuma, Mr. Chuku ya ce duka duka, 'yan Najeriyar 12 ne aka tabbatar sun harbu da wannan cuta mai saurin kisa, tuni kuma 4 daga cikin su suka rasu.
A jihar Legas kuma ana lura da wasu mutane 189, da kuma wasu su 6 a jihar Enugu domin gano ko su na dauke da cutar, sakamakon alakar da ake zaton sun yi da wadanda suka harbu da cutar na farko.
Bugu da kari Mr. Chuku ya ce Maganin Nanosilver da aka gabatarwa cibiyar yaki da cutar ta Ebola dake jihar Legas, bai samu amincewar ka'idojin bincike ba. Ya kuma musanta jita-jitar bullar cutar a jihohin Imo, da Abia, da Cross River, ya yin da ake ci gaba da nazarin rahotannin bullarta a jihar Kwara.
Shi dai Patrick Sawyer mutum da ya shigar da cutar Najeriya daga kasar Laberiya ya rasu tun a ranar 25 ga watan Yulin da ya shude, kwanaki biyar da shigar sa Najeriyar. (Saminu Alhassan)