A jawabin da ya yi, jami'in sojan bangaren Sin janar Kang Honglin ya bayyana cewa, an samu cikakkiyar nasara a ziyarar aiki da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya kawo Najeriya a watan Mayu na bana.
A yayin ziyarar, gwamnatocin kasashen biyu sun cimma ra'ayi daya kan hadin gwiwarsu ta fuskokin zaman lafiya da tsaron kasa.
A nasa bangaren, wakilin musamman na hafsan-hafsoshin sojojin ruwan Najeriya, kuma shugaban sashen tsare-tsare na hedkwatar rundunar sojan ruwan kasar manjon janar Izzi Oda a yayin jawabinsa ya nuna yabo ga nasarorin da rundunonin soja na kasashen biyu suka samu a shekara daya da ta wuce, ya kuma yi godiya ga kokarin da bangaren Sin ya yi na inganta bunkasuwar dangantakar dake tsakaninsu, yana mai fatan za a kara zurfafa da daga matsayin hadin kai a tsakaninsu. (Bilkisu)