in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfen takaita fita a Saliyo babbar nasara ce, in ji shugaba Koroma
2014-09-23 10:15:23 cri

Shugaban kasar Saliyo, Ernest Bai Koroma ya bayyana cewa, kamfen takaita fitar jama'a na kwanaki uku da aka yi wa taken "Ku tsaya gidajenku", da aka shirya daga ranar 19 zuwa 21 domin yaki da cutar Ebola, wata babbar nasara ce.

Gwamnatin kasar ta cimma nasara da kimanin kashi 80 cikin 100, in ji shugaba Koroma, tare da jinjinawa al'ummar kasar baki daya da ta ba da hadin kai da girmama sharadun da suka shafi wannan mataki.

Gudanar da wannan kamfen na da nasaba da amincewar al'ummar kasar da tsarin kiwon lafiya na Saliyo, in ji mista Koroma, ganin cewa mutane na sanar da jami'an lafiya bisa kashin kansu da mutanen dake fama da cutar Ebola, ko kuma suka mutu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China